Labaria kannywood

Alan Waka Ya Bayyana Cewar Fiya Da Shakaru 7 Ina Rubuta Wakar Yaban Manzon Allah S.A.W

Babban Mawakin Hausa Aminuddeen Ladan Abubakar, Wanda Aka Fi Sani Da Alan Waka Ya Bayyana Cewar Fiya Da Shakaru 7 Yana  Rubuta Wakar Fiyayyen  Halitta Manzon Allah S.A.W,  Wacce Ya Sanyawa Suna ” Muhammadu  Miftahul Fuluhati Linzamin Rayuwata”.

Ya kara Cewar ya kwashe shekarun ne kafin ya kammala rubuta waƙar saboda sai da ya gudanar da bincike mai zurfi, inda ya ƙara da cewa waƙar ta shafi tarihin rayuwar Annabi Muhammad (S A W) tun daga haihuwa har zuwa wafatin sa.

“Irin wannan babban aiki yana matukar bukatar bincike na tarihi da kuma irin kalmomin da za’a yi su akan Fiyayyen Halitta, don gudun zarmewa”. Inji Alan waka

Hakazalika yace ita waka “Mufitahul futuhati” littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana, inda ya ƙara da cewa babu shakka mutane sun ji dadin wakar “kuma nima Ina alfahari da ita.”

Ya ce mafiyawan wakokinsa yana gina sune kan Ilimi kuma yana gudanar da bincike kafin yayi kowacce irin waka, inda ya ce “domin yin hakan shi yake bani damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka.”

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button