Uncategorized

Amurka za ta sayar wa Najeriya makamai na dala biliyan daya

Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai na dala biliyan daya da zummar karfafa yaki da kungiyoyi masu rike da makamai.

A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce Najeriya ta bukaci sayen jiragen helikwafta 12 masu kai hare-hare da makami mai kai hari inda aka nufa ba tare da matsala ba.

ALSO CHECK:  Phyno – Ikepentecost ft. Flavour

A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce Najeriya ta bukaci sayen jiragen helikwafta 12 masu kai hare-hare da makami mai kai hari inda aka nufa ba tare da matsala ba.

Amurka ta ce daga yanzu Najeriya ba za ta fuskanci wata matsala ba wajen sayen makamai daga wurin ta.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito sai dai ana sa rai wannan batun zai dauki akalla shekaru biyar kafin a kammala shi  domin kuwa zai hada da horas da dakarun tsaron Najeriya kan yadda za su yi aiki da makaman da kuma kauce wa kai hari kan fararen-hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button