NEWS

BIDIYO: Shugaban kungiyar kungiyar Izalah a Najeriya ta ya yi Allah wadai da abinda ya faru a jihar Sokoto

Shugaban Izalah Ya Yi Allah Wadai…

Shugaban kungiyar kungiyar Izalah a Najeriya ta ya yi Allah wadai da abinda ya faru a jihar Sokoto.

Bala Lau yace hukuma ce ke da hurumin yanke hukunci ga wanda ya zagi Annabi, ba ‘dai’daikun mutane ba.

Ya kuma yi kira ga Hukumomi da su dinga zartar da hukuncin kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) kafin jama’a su kai ga nasu hukuncin, Wannan ne kadai zai hana’dai’daikun mutane daukar mataki na kisa.

A jawabin da kungiyar ta saki, ta ce yarinyar ta kunduma ashariya ga Annabi (SAW) wanda duk musulmi bazaiji dadi ba, wanda hakan har yakai ga wasu jama’a suka kasheta kuma suka kona ta.

“Addinin musulunci bai bada dama ga musulmi ya zagi ko wane Annabi daga Annabawan Allah ba,

Also check: Waje – Vibes Ft. Falz Mp3 Download

dan haka akwai bukatar shugabannin kiristoci su dauki aniyar wayar da kan mabiyansu akan illar taba mutunci ko zagin fiyayyen halitta wanda hakan ka iya tayar da husuma a cikin kasa.”

Shugaban Izalah, Sheikh Bala Lau, yayi kira na musamman ga hukuma da ta dinga saurin daukan mataki na kisa ga wanda ya zagi Annabi (S)

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button