NEWS

Buhari zai taimaka wa Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga da kuma haɗin kan ƙasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin da yake karɓar baƙuncin wakilin Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

“Za mu duba halin da kuke ciki don ganin yadda za mu taimaka,” IN JI Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Fe mi Adesina ya fitar.

Also check: BIDIYO: Shugaban kungiyar kungiyar Izalah a Najeriya ta ya yi Allah wadai da abinda ya faru a jihar Sokoto

Wakilin na musamman, Albino Matham Ayuel, ya yi wa Buhari bayani kan yadda wata ƙungiyar masu ta da ƙayar baya “kamar Boko Haram ɗinku ta aikata kashe-kashe kuma ta wulaƙanci da lalatawa”.

Sanarwar ta ƙara da cea daga baya kuma ya nemi “haɗin gwiwa kan tsaro, musamman ba wa dakaru horo tun da kuna da ƙwarewa kan wannan lamari”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button