NEWS

Hisbah Ta kama Mutum Saboda Ya Gina gida ‘da Shafukan Ƙur’ani’ a Kano

Hukumar Hisbah mai tabbatar da bin dokokin Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta ce ta kama mutum uku da ake zargi da yin amfani da shafukan Al-Ƙur’ani mai girma wajen gina wani gida a unguwar Gaida da ke jihar.

Mataimakin kwamandan hukumar mai kula da ayyuka na musamman na, Ustaz Usaini Usman Cediyar ‘Yan-Ƙuda, ya faɗa wa BBC Hausa sun kama mai gidan tare da malamin da ake zargin shi ne ya sa shi amfani da shafukan wajen yin gini.

Ya ƙara da cewa a lokacin da jami’ansu suka isa wurin da ake ginin sun tarar da wasu daga cikin takardun ɗauke da rubutun wani ɓangare na Ƙur’ani.
“Tuni mutanen unguwar suka yi gaban kansu suka rushe ginin,” a cewarsa.

Sai dai ya ce wadanda ake zargi sun shaida musu cewa shuna amfani da shafukan ne a wajen yin ginin saboda tsaro.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button