Labarai

Idan Na Zama Shugaban kasa Yajin Aikin ASUU Zai Zama Tarihi~ Kwankwaso

Dan Takarar shugaba kasa Na Jam’iyyar NNPP,  Sanator Rabiu Musa Kwankwaso  Ya Ce Daya Ranar Da Ya Zama Shugaban kasa An Daina Yajin Aikin Malamin Jami’o’i A Nijeriya.

Kwankwaso Wanda Har ila Yau  Tsohon Ministan Tsoro Ne Kuma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Ya Bayyana Hakan Nan A Wata Hirar Ta Musamman Da Manama Labaria A Gombe, Idan Ya Ce Da Zarar An Zabe Shi Malamin Jama’a Za Su Daina Kuka.

Yace In Ban Da Hakar Siyasa Da Ya Shiga Da Yanzun Shi Farfesa Ne, Inda Ya Ce Jama’a Malamin ‘ Yan Uwansa Ne Zai Zauna Da Su Ya Saurare Su.

” A Siyasar Ma Ni Ba Irin Wanda Za A Tambaya ina Satifiket Dinsa Bane Ya Tsaya Kame- Kame Ko Ya Ce Ya Bata Ba Ne,” Inji Kwankwaso.

Ya Kuma ce bangaren da zai bai wa fifiko shi ne na ilimi kama duk wanda ya san kano Lokacin yana Gwamna ya san ya bar tarihi a jihar wajen inganta fannin.

A Cewarsa, ba zai Kwashe kudin Nijeriya don biya musu bukata ba, zai duba matsalar ce tun daga farko ya dakile ta, yana mai cewa ba zai bari a kwashe ba dole sai da dalilin abin da za a yi da kudi.

Yace idan ya zama shugaban kasa, duk wani azzalumin zai kama shi ya kai gidan gyaran hali ya gyara halin sannan a fito da shi.

Daga nana sai dan takarar ya yi kira ga Malamin Jami’o’i da su yi wa Allah da Manzonsa su koma Aji don gwanatin ba kallon su za ta yi ba.

Source: Amaryar hausa.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button