Labarai

Innalillahi: Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mijin Da Matarsa, Wadanda Dukkansu Likitoci Ne

Wata Gobara Da Ake Kyautata Zaton Man Fetur Ne Ta Barke, Ta Yi Sanadin Mutuwar Wasu Ma’auratan Likitoci, Dokta Auta Gidado da kuma Dakta Amina Ahmad.

Har Zuwa Rasuwarsu, Dukkansu Sun Yi Aiki Da Jami’ar Maiduguri Teaching ( UMTH) Da Ke Jihar Borno, kamar Yadda Jaridar City & Crime Ta Ruwaito.

An Tattaro cewa lamarin ya faru ne safiyar lahadi a wani gida da suke zaune a kan titin Legas, Maiduguri.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gobarar wacce ta yi kamari ta fara matar kuma a kokarin kubutar da ita mijin ya kone sosai sannan aka garzaya da su UMTH, amma Dr Auta Gidado ya rasu da sanyin safiyar Talata.

Majiya ta ci bayyana cewa an yi jana’izar marigayi Dr Auta kamar yadda hakkin

addinin Musulunci ya tanada bayan sallar jana’izar a masallacin UMTH.

Majiya ta  ci gaba cewa, “Ba a yi sa’o’i 24 da rasuwar mijinta ba, mun kuma yi rashin

Dakta Amina Ahmad da safiyar. Mu samu sakon ne da misalin karfe 3 na safe”.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, shugaban kungiyar likitocin da ke UMTH,  Dr Abdullahi Usma.

Ya Ce, ” Eh, mun rasa su duka biyun daga barkewar gobara, A yayi  da magana, babu

wanda zai iya gaya muku cikakken bayani,  amma abin da ake ce mana shi ne gobarar ta

tashi ne daga man fetur “.

Allah Ya Jikan Su Da Rahama Ameen.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button