Labarai

Innalillahi: Yadda Rijiya Ta Rufta Da Uba Da Dansa A kano

A yau mun samu rahoton wani dattijo mai shekaru 60, mai suna Malam Bala da dansa,  Sunusi Bala mai shekaru 35, sun mutu a cikin wata rijiya da ke Sabon Garin Bauchi a karamar hukumar Wudil a jihar Kano.

A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, lamarin ya faru ne a ranar Laraba bayan kiran Malam Bala da Dansa don su yashe wata Rijiya.

A Cewarsa, mahaifin da dansa sun yi nasarar yashe rijiyar, amma dan ya makela a ciki sabida rashi Iska, wanda hakan ya tilasta wa mahaifin yunkurin kubutar da dansa, amma abin takaici shi ma rashin iskar ya sake makalar dashi.

Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Wudil da misalin

karfe 11:30 na safe daga wani Isma’ila Idris cewa wasu mutane biyu sun makale a cikin

rijiya kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da

misalin karfe 11:33 na safe.” Inji Abdullahi.

Ya kara da cewa, an fito da wadanda abin ya rutsa da su daga cikin rijiyar, daga bisani

kuma aka tabbatar da mutuwarsu, an mika gawarwakin su ga Insifeto Felix Gowok na ofishin ‘yan sanda na Wudil.

Dan fatan Allah ya gabata musu Ameen..

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button