Labarai

kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi Daurin Shekara Daya A Gidan Bisa Laifin Satar Akuya

A yau zamu kawa muku Labarin Yadda wata Kotun ta yanke wa wani matashi dan  Shekara 23, Sadiq Mikko, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar akuya, da kudin ta ya kai Naira 40,000.

Miko, wanda ke zaune a Tudun Murtala Quarters kano, an same shi da laifin sata.

Alkalin kotun, Zabairu Inuwa, ya baiwa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar Naira

30,000 bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Inuwa ya kuma umarci mai laifin da ya biya wanda ya shigar da karar kudi Naira 40,000 a

matsayin diyya na akuyar ko kuma ya yi zaman gidan yari na watanni tara.

Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Ahmad saki, ya shaida wa kotun cewa wani

Isah Bello na unguwar Ranji kano na ya kai karar a ofishin ‘ yan sanda na Gwagwarwa kano a ranar 10 ga watan Yuli.

Saki ya ce a wannan ranar, da misalin karfe 10 ne safe, wanda aka kara ya sace akuya

wanda ta kai Naira 40,000 a gidansa da ke Ranji kano.

Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 287 na kundin laifuffuka.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button