Labaria kannywood

Rashin tsaro: Rarara Ya Shirya Addu’a Ta Musamman a Kano

Shahararren mawakin siyasar nan na Hausa, Dauda Adamu Kahutu, wanda a ka fi sani da Rarara, ya shirya addu’a ta musamman a kan rashin tsaro da ke addabar Arewaci da ma wasu sassa na Nijeriya.

An shirya addu’ar ne a Jihar Kano a yau Litinin, da zimmar Allah Ya kawo ƙarshen rashin tsaro a ƙasar.

Da ya ke jawabi a yayin taron addu’ar, Rarara ya ce ya zama wajibi a haɗu a yi wa ƙasa

addu’a a bisa mawuyacin halin da ta tsinci kanta.

A cewar sa, rashin tsaron da ya addabi Arewa da ma wasu sassa a ƙasar nan, na

matukar bukatar addu’a, musamman ma yadda babban zaɓe na 2023 ke tunkaro wa.

Ya ƙara da cewa Musulmai da Kiristoci ya kamata su duƙufa da addu’a a masallatai da coci-coci domin neman ɗauki daga Ubangiji.

Rarara ya kuma ce taron bashi da wata alaƙa da siyasa, “illa dai a nemo mafita a wajen Ubangiji domin samun zaman lafiya.

“Idan babu zaman lafiya, ko mu ma ba za mu iya yin harkar fim ɗin mu ba. Saboda haka

muna kira ga ƴan Nijeriya, Musulmai da Kiristoci, da mu dage da addu’a a masallatai,

coci-coci da kuma gida-gida domin Allah Ya bamu zaman lafiya,”in ji Rarara.

Ya kuma ƙara da cewa taron ya yi amfani wajen kara danƙon zumunci tsakanin ƴan masana’antar Kannywood.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button