Labarai

Sarki Daura, Mai Shekaru 90 Ya Sake Aure Budurwa ‘ Yar Shekara 22

Sarki Daura, Alhaji Dr Umar Faruk mai shekaru 91 ya sake yin Wuf da budurwa dunya shakaf mai shekaru 22.

Majiyarmu da ta nemi a sakaya sunanta daga garin na Safana inda aka dauro auren ta ce, da fara neman auren da yin komai an yi shi ne cikin sati guda.

Kazalika, an yi auren ne tamkar a asirce domin babu wani shagalin bikin da aka yi.

Ita dai A’isha, amaryar Sarki, ’ya ce ga Alhaji Yahuza Gona, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Safana a lokacin da aka taba yin zaben kananan hukumomi ba tare da jam’iyya ba.

Tuni dai amarya Aisha Gona Safana ta tare a dakinta inda ta tabbata sabuwar gimbiya kuma amaryar tsohon basaraken.

Wane fata za ku yi musu?

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button