NEWS

Shugaban APC Bai Hakura Ba, Zai Gabatar Da ɗan Takarar Da Yake So Ga Buhari, Kalu.

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a APC, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu, da kwamitin gudanarwa NWC zasu gabatar da Lawan ga Buhari.

PUNCH ta ruwaito cewa Adamu da sauran yan kwamitinsa na NWC zasu kai wa Buhari sunan Ahmad Lawan ne domin ya goya masa baya a matsayin ɗan takarar maslaha.

Rahoton da ya karaɗe kafafen watsa labarai ya nuna cewa Adamu ya zaɓi shugaban majalisar dattawa a matsayin ɗan takarar sulhu yayin da zaɓen fidda gwani zai gudana yau Talata.

Bayan haka ne, Mambobin NWC da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, suka fito suka shaida wa duniya cewa ba su da hannu a zaɓen ɗan takarar maslaha.

Sun jaddada cewa dukkan yan takara zasu haɗu a akwatin zaɓe yayin da Deleget zasu raba gardama kan wanda zai karbi tutar jam’iyya a babban zaɓen dake tafe.
Daga jaridar hausa.legit.ng na ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button