Al'ajabi

Ta Raba Harshenta 2 Don Dandana Pepsi Da Koka-Kola Lokaci Guda

Wata mawakiya mai suna Brianna Mary Shihadeh mai sha’awar gyaran jiki wadda ta raba harshenta biyu ta bayyana yadda za ta iya dandana abubuwa biyu daban-daban a lokaci guda.

Hakan dai ya sa mutane suka yi mamakin irin fasaharta wajen bambance dandano da harshenta da ta raba.

A kwanakin nan ta bar mutane cikin mamaki bayan ta dandana ruwan lemon biyu a lokaci guda, inda ta sa rabin harshenta a cikin kowane kofin gilashi.

Bayan da aka wallafa bidiyon Brianna Manhajar TikTok wanda ya dauki hankalin jama’a sosai, Brianna, wacce ke zaune a Kudancin Jihar Kalifoniya a Amurka, bidiyonta ya samu sharhi da ra’ayoyin mutum 293,000, tare da sanya mabiyanta farin ciki.

A cikin dan lokaci idan an yi la’akari da ra’ayin jama’a game da muhawarar da dandana lemon Pepsi da Koka-Kola, Brianna ta yi, watakila ya zama abu mai rikitarwa, inda ta tabbatar da cewa, ‘za ta iya dandana bambanci tsakaninsu lokaci guda.

Brianna – wacce ke da adireshin @flowerfriendly ta gudanar da gwajin dandanon gishiri da zaki, inda ta raba harshenta a tsakanin gilasan ruwan sukari daya da wani mai dauke da ruwan gishiri.

Da take waiwayar irin wannan haduwar dandanon, Brianna ta ce, a bar kwakwalwarta haka ba ta cikin rudani. An bar masu amfani da TikTok cikin mamaki bayan sun shaida kwarewar Brianna da ba kasafai ba ne ake iya samun hakan, wasu sun yaba bidiyonta da cewa ya kasance “mai gamsarwa.”

Wani mutum ya ce: “Ban taba tunanin yin amfani da wannan ba! Kina da ban-mamaki. Ba zan iya daina kallo ba.”

Labarai na daga jiridan Aminiya Hausa

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button