Labarai

Tirkashi: Miji Na Ya Gudu Tare Da Budurwarsa, Mata Mai Neman a Raba Aurenta Ta Fada Wa kotu

Wata Kotu da ke Jos ta tsakiya ta amincin da rokon wata matar aure, Rhoda Jonathan da ke neman a raba aurenta bisa hujjar cewar mijinta, Dakogol ya gudu tare da budurwarsa.

Jonathan a takardar neman a raba auren nata, ta yi Zargin cewa Dakogol na yawan Zagin ta kuma ya kasa biyan bukatun Iyalinsa.

Alkalan da suka jagoranci shari’ar, sadiq Adamu da Hyacenth Dolnanan, a wajen amincinwa da rokon da Jonathan ta gabatar, su ce, ” duk kokarin sulhunta ma’aikatan ya ci tura.”

Alkalan sun umarci mai kara da wanda ake kara su rabu da juna kawai.

Sai dai kotun ta umarci Dakogol da ya rika bayar da kudin rainon ‘ya’ yansa duk wata.

Tun da fari, Jonathan ta roki kotun ta da raba aurensu, inda ta ce mijin nata da su ke tare tsawon shekaru 20, ya kasa kula da ‘ ya’ yansu uku.

Kafin ya gudu, watanni hudu da suka gabata, muna yawan samun sabani, har ta kai ga ya daina sauke hakkisa a matsayin mijin na.

” Na gaji kuma ina so in ci gaba da rayuwata, ” in ji ta.

Allah ya kyautaa Ameen..

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button