Labarai

Uwargida Ta Nemi Saki Akan Sha’awar Jima’i da ‘Da Ba A Saba Ba’ Mijinta

A yau mun samu rahoton aka Wata Matar Aure Mai suna Zainab Yunusa ta roki kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna da ta raba aurenta da mijinta, Ali Garba, bisa bukatarsa ta jima’i da ba a saba gani ba.

Mai shigar da karar ya shaida wa kotun a ranar Laraba cewa Mista Garba ya bukaci yin

jima’i ko da tana cikin jinin haila da kuma lokacin azumin Ramadan. Kamar yadda Daily Nigeria ta rawaito

Ms Yunusa ta ce sun zauna tare tsawon shekara guda a matsayin ma’aurata, ta kara da cewa ta koma gidan iyayenta kan lamarin.

“Lokacin azumin Ramadan, yakan dawo gida da rana yana neman yin jima’i, duk lokacin da na ki, sai ya yi fushi, kuma yana jin haushi.

“Kuma idan na tambaye shi abinci, yawanci yakan amsa cewa in je in hadu da saurayina ya ciyar da ni.

“Bai taba yarda da ni ba har bai taba barin wani da ya hada da ‘yan uwana maza ko

mata su ziyarce ni ba,” kamar yadda ta shaida wa kotu.

Matar ta ce ta gudu daga gidan aurenta, saboda ba za ta iya gamsar da mijinta na sha’awar jima’i ba.

Don haka, ta roki kotu da ta raba auren, domin ba ta shirya kai wa mijinta wani bukatu na jima’i da saba wa Allah ba.

Sai dai mijin ya musanta zargin, inda ya ce Yunusa ya shigar da kara a gaban kotuna da dama a kansa.

Mista Garba, ya shaida wa kotun ta bakin lauyansa, M.A Sambo, cewa mahaifiyar

matarsa ta je gidansa ba ya nan, ta kwashe kaya tare da sayar da kadarorinsa, kafin ta tafi da diyarta.

Ya ce mahaifiyar ta yi alkawarin mayar da duk abin da suka kwaso daga gidansa a yayin wani taron sulhu.

Ya jera abubuwan da aka cire sun hada da kujeru na Naira 100,000, talabijin, firij guda

biyu, faranti na Naira 35,000 da sauran kayayyakin kicin, yadi 20 na kafet na fata da

kuma katifa na Naira 15,000.

Malam Garba ya roki kotu da ta duba bukatarsa ta a mayar masa da kadarorinsa a

matsayin wani sharadi na amincewa da bukatar saki.

Alkalin kotun, Murtala Nasir, bayan ya saurari dukkan bangarorin biyu, ya umarci mai kara

da ta zo kotu tare da mahaifiyarta a rana mai zuwa.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba, domin ci gaba da sauraren karar.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button