Al'ajabi

Wata Budurwa Ta Shirya Tsaf Don Auren Kanta A Indiya

Wata Budurwa mai suna Kshama Bindu ta shirya tsaf don shirin ‘auren kanta’ a yadda ta Shirya fara gudanar da bikin gargajiya na Hindu wanda zai gudana a yammacin ranar 11 ga Yuni, 2022 a wani gidan ibada a birnin Vadodara, a yammacin jihar Gujarat, Indiya.

Amarya ta sha ado cikin jajayen kayanta na amarya, da kyakkyawan lallanta a hannunta da hoda sanye cikin gashin kanta, amarya za ta yi zagaye wuta ta Alfarma sau bakwai na al’ada kamar yadda amarya da ango suka saba gudanarwa a al’adar kasan in za suyi aure.

Daga bisani kuma, za a gudanar da shagulgulan biki kamar shafawa amarya hodar tumeri da raye-raye da kade-kade, bayan Kammala shagulan biki, amarya za ta Ziyarci gidan Gao Inda zata kwashi hutun sati biyu don shan Amarci.

Irin wannan aure, wanda zukekiyar Budurwa za ta auri Kanta, shine na farko a tarihin kasar indiya.
Irin wannan rayuwa, ta samo asali ne cikin ‘yan shekarun da suka gabata daga mutanen yankin Yammacin Duniya (Turawa), yanzun kuma lamarin gashi ya iso gabashin Duniya (Indiya).

Source Leaderships Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button