Labarai

Watan Budurwa Wazamiya Ta Bayyana Idan Ta Yiwa Yara 80 Kaciya Tun Tana shekara 17 A Duniya

Hassana Gambo Dakata, matashiya mai shekaru 17 da Haihuwa a duniya wacce ta gaji sana’ar wanzanci daga mahaifinta ta bayyana cewa ta yi wa yara 80 kaciya a shekarunta 17 a duniya.

Ta bayyana cewa yanzu haka ta kware wajen iya cire belu da aski da yi wa yara kaciya.

An dai nada ta a matsayin mataimakiyar mata wanzamai ta yankin Dakata a karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, inda Sarkin askan Dakata, Alhaji Hassan Zakari ya nada ta a cikin sarautu biyar da ya nada a ranar Lahadi da ta gabata a Unguwar Dakata ta Kano.

Sauran sarautun da sarkin askar Dakata ya nada a wannan rana akwai Nafi’u Ibrahim, a matsayin Galadima da Bilyamunu Lawan, a matsayin majidadin sarkin askar Dakata da Abubakar Dan Baffa, a matsayin waziri da Hassan Gambo Dakata, mai aski Damagun, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar wanzamai na karamar hukumar Nasarawa na Jihar Kano.

A jawabinsa, Alhaji Hassan Zakari ‘Yan ya ce ya nada wadannan sarautu ne don bunkasa sana’arsu mai daraja da tarihi kuma wanzami na asali baya rainuwa a kan abin da aka ba shi na aiki, ciniki ko rainuwa ba na wanzamin arziki ba ne.

Ya ce daukacin wadanda aka nada sun yi alwashin yin biyayya da bayar da gudunmawa ga sarkin askar Dakata da na karamar hukumar Nasarawa da kuma Kano baki daya.

Source: Leaderships Hausa 

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button