Labarai

Yadda An Kori Wata Musulma Daga Sakatariyar Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) Saboda Ta Sanya Kaki Mai Launin Siket Maimakon Wando

Bidiyon wata ‘yar bautar kasa Musulma wadda aka kore ta daga sakatariyar NYSC saboda yanayin shigarta wanda ya saba wa ka’idar NYSC, ya karade yanar gizo. Jiridan Rariya Ta Ruwaito.

A bidiyon cikin yaren Yarbanci an ga wata ma’aikaciya a sakatariyar tana korar yarinyar da ta keta ka’idojin NYSC, inda ta nemi ta bar wurin.

Ana ganin matar tana tambayar sauran ’yan bautan kasar ko a lokacin da suke sansaninsu, an ba su damar yin hakan, inda akasarinsu suka amsa da cewa a’a.

Sa’ad da yarinyar ta yi ƙoƙari ta kare kanta, babbar matar ta yi mata tsawa kuma ta neme ta da ta sami izini daga Ko’odinetan Jihar don yin suturar da ta yi.

Bayan faruwan hakan matan da ake tunani kamar ita ce shugabar su a matakin karamar hukuma ta koma ofishinta yayin da ta bar yarinyar a tsaye a wajen.

Saidai babu tabbacin ko a wace jihar lamarin ya auku, amma an matar tana y8 wa yarinyar Yarbanci.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button