Labarai

Yadda Wani Tsoho Ya Auri Jikarsa Yaki Kuma Yarda Ya Sake Ta

Wani Tsoho, Alhaji Musa Tsafe dake Karamar Tsafe a jihar Zamfara, Ya ki amince wa ya saki wata jikarsa da ya aura tsawon shekaru 20.

Alhaji Musa ya yanke shawarar kin sakin jihar tasa ce mai suna wasila Isah Tsafe ‘ Yar Shekara 35 bayan an sanar da shi cewa auren na su haramatacce ne.

Matar tasa, Wasila Tsafe, ta haifar wa Alhaji Musa ‘Ya’ya 8.

An rahoto cewa, an sanar da Masarautar Tsafe kan maganar aure, inda dattawan afadar suke yiwa Alhaji Musa kiranye, bayan gudunar da bincike aka sheda wa Alhaji Musa cewa, auren na sa da jikarsa bisa sharudan addinni Musulunci haramatacce ne.

Hakazalika, Malaman addinin Musulunci sun shawarar Musa ya saki jikarsa da yake auren, Wasila  Tsafe amma lamarin ya cutura ga Alhaji Musa Inda Yace hakan ba za ta sabu ba.

Biyo bayan tirjiyar da Alhaji Musa ya yi, Hukumar Hisbah ta karamar Hukumar Tsafe ta maka Alhaji Musa kara a gaban Babbar Kotun Shariar Musulunci Dake Jihar Zamfara .

Kotun ta sa ranar 21 ga watan Yulin 2022 ranar sauraron karar.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button