NEWS
Yanzu-Yanzu: Amosun Ya Janye Daga Takarar Shugaban kasa Na Jam’iyyar APC Ga Tinubu
Wani tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya janye daga takarar. Daily Nigerian na ruwaito.
Mista Amosun ya bayyana ficewar sa ne a lokacin da yake jawabi ga wakilai a babban taron jam’iyyar APC na kasa a ranar Talata a Abuja.
Ya umurci magoya bayan sa da su zabi Bola Tinubu a wajen taron.
A baya dai tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio ya janye daga takarar inda ya bukaci magoya bayansa da su zabi Mista Tinubu.