Labarai

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Hana Amfani Da A Daidaita Sahu Daga Karfe 10 Ne Dare

Gwamantin jihar kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dakatar da amfani da babur mai kafa uku da aka fi sani da A daidaita sahu a jihar daga karfe 10:00 na dare a fadin jihar, daga ranar Alhamis mai zuwa 20 ga watan Yulin da muke ciki. jiridan BBC Hausa ta rawaito.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar ya ce an dauki matakin ne yayin zaman majalisar tsaro ta jihar.

Ya ci gaba da cewa matakin zai taimaka wajen tabbatar da kiyaye rayuka da dukiyoyin al’iumar jihar.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga direbobin baburan da su tabbatar da bin wannan sabuwar doka.

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button