NEWS

Yanzu – Yanzun: An Kashe Wani Musulmi Saboda Batanci Ga Annabi A Abuja

An Abuja – wasu matasa a ranar Asabar sun hallaka wani Dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batancin ga Manzon Allah ( S.W.A) a birnin tarayya a Abuja.

Shaidun gana ido sun bayyana cewa, wanda aka kashe din musulmi ne, kuma wannan ba shi ne farau ba domin an san shi da laifin cin

 

mutuncin manzon Allah, inda na baya-bayan nan ya faru da tsakar daren ranar Asabar.

Sai dai bayanai sun ce an dauki matakin ne da misalin karfe 1 na ranar Asabar bayan ya yi kokarin neman mafaka a ofishinsu na ‘yan banga da ke kasuwar.

 

An tattaro cewa jama’ar da suka fusata sun ci karfin jami’an tsaron yankin, wanda a dalilin haka suka samu nasarar kashe shi a gaban ofishin, sannan suka kone shi.

“Muna san mutumin wanda ake kira Small Hundaru, wannan ba shi ne karon farko da ya zagi Annabi ba kafin a dauki matakin,” in jiHalilu, wani mai sana’a a kasuwar.

 

“An kama shi ne bayan ya sayi abinci a kasuwa da rana, domin a lokacin da aka yi wannan batancin mutane kadan ne a wurin, sai aka yi amfani da sanda aka buga masa kai. Duk da cewa yana da bindiga a tare da shi, an kwace ta kafin a yi masa jina-jina.

 

“Bayan haka, sai aka rika jifansa da duwatsu kafin ya garzaya ofishin, amma abokan aikinsa a ofishin da suka san ba za su iya kare shi ba saboda yawan mutanen da suka biyo shi, dole suka zuba ido suna kallo.

Asali daga Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button