NEWS

Yanzu-Yanzu:Yadda Hatsarin Tankar Mai Ya Lakume Rayuka A Zariya

Wannan hatsarin tankar mai ya auku ne a Gadar Dan Magaji da ke Wusasa, Zariya, da misalin karfe shida na safiyar Alhamis,

kamar yadda Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) Reshen Zariya, Abdurrahaman Yakasai. Daga jiridan Aminiya Hausa.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur na Kasa (IPMAN) Reshen Jihar Kaduna, Maiwada Zariya, ya ce motar mailamba RNG 065 XA (Jigawa) ta taso ne daga Legas zuwa Kano dauke da litar mai kusan Dubu arba’in da biyar.

 

Ya ce hatsarin ya aukune bayan direban tanakar man ya kauce wa wani direban motar bas mai tukin ganganci da ya daukokaji, a garin kaucewa nauyin tankar ya rinjaye ta, ta fadi, ta kama da wuta.

 

Zuwa lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, ya ce, ba a kai ga gano mutanen da hatsarin ya rutsa da su ba, amma an kaigawarwakinsu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.

 

Maiwada Zariya ya bayyana cewar tanakar ba ta danne kowa ba kamar yadda ake yada jita-jita cewa ta danne wadansu almajirau masu wucewa.

 

Ya ce, “Yazu haka mun sami nasarar daga takar kuma babu kowa a karkashinta, sai dai wutar motar ta kona shaguna da ke kusa da wurin kuma a lokacin masu shi ba su isa budewa ba.”

Kucigaba da bibiyar shafinmu mai tare alibaka Naijasmart domin samu labarai mugode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

 
Back to top button